Yadda Ake Ajiye Photo, Video Ko Takardu A Email/gmail Ta Yadda Ba Zaka Taba Rasa Su Ba

Assalamu alaikum barkanmu da sake kasancewa daku a wannan shafin namu mai Albarka na Hikimatv.com

Darasin mu na yau zanyi bayani akan yadda zaku ajiye Photo, ko videos kokuma wasu takardu akan Gmail dinka ta yadda ba zaka taba rasa suba ta hanyar amfani da wani application mai suna Drive ko ince Google Drive.

Google Drive: wata ingatacciyar ma’adana ce da kamfanin google ya tanadarwa duk wanda ya mallaki account din ‘Gmail’ kuma kyauta ne. G-drive wato google drive ya kan ba da damar ajiya na kimanin wurin ajiya 15GB (storage space) 15GB, sannan kuma google ya tsare maka shi, wato ya ba da tsaro (security) ingantacce.

An samu cigaba sosai a duniya, an hutar da mutane game da yawo da takardu, mutukar ka mallaki email to za su ba ka damar ajiya a wannan ma’ajiya ta google drive. Sannan kuma idan ka ajiye kayanka a google drive har dal ba zai bata ba, haka kuma ba zai lalace ba.

Karanta Ga Wata Sabuwar Dama Ta Samu: DanGote Zai Dauki Matasa 300,000 Aiki A Fadin Nigeria

Google Drive yakan iya adana bayanai iri-iri, kama daga rubutu (document), murya (audio), hotuna (pictures) da kuma bidiyo (video)

Yadda Zaka Gano Google Drive na kan Wayar ka:

Mafi yawancin wayar hannu kirar (smartphones) tana zuwa da shi kuma kyauta yake a cikinta. Idan aka duba wayar da kyau cikin nutsuwa za a ga application din me suna Drive.

Idan kuma baka sameshi akan wayar kaba saika danna Link dake kasa domin Saukar dashi

Download Google Drive

Bayan kayi download dinsa sai kayi install dinsa sannan saika budeshi domin fara amfani dashi

Daka bude shi saika duba daga sama a gefan dama akwai wani icon na mutun saika taba wajen anan zai baka damar dora gmail dinka wanda kakeso kayi amfani dashi.

Bayan ka dora gmail din, yanzu saika duba daga kasa gefan dama zakaga Alamar + saika danna da zarar ka danna zakaga abubuwa kamar haka:

Folder

Upload

Scan

Google Docs

Google Sheets

Google Slides

Yadda ake ajiya a google drive shi ne, da farko za ka bude upload, nan take zai bude maka local storage, wato abubuwan da ke cikin wayarka (memory). Da zarar ya bude, sai a zabi abin da ake so a ajiye din.

Page wanda yake dauke da abubuwan da aka ajiye a cikinsa zai bayyana. Shi kenan an yi ajiya a cikin google dribe din, duk lokacin da ake bukata sai a yi amfani da shi.

Wani lokacin idanan ajiya (upload) sai ya nuna waiting for Wi-Fi. To hakan yana faruwa ne musamman idan wannan ne lokaci na farko da mutum ya fara amfani da google dribe din. A wasu lokutan kuma idan ana da matsalar network (data) ana fuskantar hakan.

Idan aka yi upload, sai a ga yana nuna waiting for Wi-Fi, to ga yadda za a yi masa. A saman wayarka akwai wasu layuka guda 3 a kwance daga gefen hagu (option) kusa da Search in Dribe, za a ga wani feji zai bude sai a danna Settings. Zai kara bude wa, to daga can kasa an rubuta ‘Data Usage’ a gefen rubutun akwai wani digo shudi (blue) sai a danna. Shi kenan wannan matsalar an yi maganinta.

Akwai abubuwa masu yawa wadanda google dribe kan iya taimaka wa wajen yin amfani da su. Google Dribe yana ba da damar ajiyar kowane irin file kamar yadda na muka ambata a baya. Za a iya adana file komai girmansa idan bai wuce nauyin 15GB ba.

Muhimmancin Google Drive

Karanta Har Yanzu Ana Iya Cike Tallafin Rancen Kudi Daga Gomnati Ga Jerin Rancen Kudin Da Har Yanzu Suna Tafiya

Kadan daga cikin muhimman amfaninsa shi ne:1) Upload: Yadda za a dora abu a kan google dribe, kamar yadda na kawo misali a baya.2) Scan: Goigle dribe ya kan ba da damar yin scanning na takardu masu mahimmanci, kamar na karatu kuma a adana shi a cikin dribe, kuma ya kan ba da damar yin amfani da su a duk lokacin da ake da bukatarsu.

Kamar a wajen rijista ta yanar gizo, lokuta da dama a kan bukaci takardun kamala karatu ta hanyar tura wa a website na neman aiki ko scholarship da sauransu. Scan yana taimaka wa sosai wajen kiyayewa hadarin gobara, ruwa da abubuwa makamantansu da kan iya kawo lalacewar takardu ko batansu.

Idan kana da google dribe babu kai ba yawo da takardu a hannu.3) Folder: Folder tana taimaka wa wajen rarrabe files da aka adana.

Shin Ana iya Gara Girman Ma’ajin Google Drive?

Mutum idan yayi ra’ayi zai iya kara girman wannan ma’ajiya ta google drive daga daga 15GB zuwa 100GB,150GB, 200GB zuwa sama da hakan amma wannan siya ake yi, wato sai ka yi upgrade na google drive din naka.

Allah ya bada sa’a

Advertisement Join Our Whatsapp Group Join Our Whatsapp Group

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button
error: Alert: Content selection is disabled!!