Muhimmiyar Sanarwa Ga Wanda Sukayi Register na Katin Zabe Voter’s Card

INEC Za Ta Shafe Kwana 40 Tana Rabon Katin Rajistar Zaɓe, Daga Ranar 12 Ga Disamba

Hukumar Zaɓe ta Ƙasa (INEC) ta ce za ta shafe kwana 40 ta na rabon katin shaidar rajistar zaɓe (PVC), daga ranar Litinin, 12 ga Disamba.

Kwamishinan Yaɗa Labarai na INEC, Festus Okoye ya ce a cikin wata sanarwa za a ci gaba da aikin raba katin har zuwa ranar Lahadi, 22 ga Janairu, 2023.

Ya ce daga ranar 6 zuwa 15 ga Janairu, 2023, za a koma ana rabawa a mazaɓu 8,809 na faɗin ƙasar nan.

Ya ce: “Amma daga ranar 15 ga Janairu, za a koma rabon katin a ofisoshin INEC da ke ƙananan hukumomi 774 na faɗin ƙasar nan. Za a ci gaba da rabon har a ranar 22 ga Janairu, 2023.”

Okoye ya ce za a fara rabon katin tun daga ƙarfe 9 na safe har zuwa ƙarfe 3 na yamma, a kowace rana, har da ranakun Asabar da Lahadi.

Ya ƙara da cewa kwamishinonin zaɓe na jihohi za su gana da masu ruwa da tsaki da su ka haɗa da sarakunan gargajiya da sauran masu riƙe da sarautu, malaman addini, ƙungiyoyi da kafafen yaɗa labarai domin su sanar da su irin tsare-tsaren da za a yi domin tabbatar da an yi rabon katin shaidar rajistar zaɓen a cikin ruwan sanyi, kuma cikin nasara.

Za a yi zaɓen shugaban ƙasa da na Majalisar Tarayya a ranar 25 ga Fabrairu, 2023.

Advertisement Join Our Whatsapp Group Join Our Whatsapp Group

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button
error: Alert: Content selection is disabled!!