Hukumar Zabe Ta INEC Ta Fara Tura Sakon Training Ga Wadanda Suka Cike Aikin Zabe

Assalamu alaikum jama’a barkanmu da sake kasancewa daku a wannan shafin namu mai albarka na hikimatv.com

Kamar de yadda kuka sani Hukumar zabe ta kasa mai zaman kanta, wato INEC ta fara tura sakon training ga wadanda suka cike aikin

Hukumar zabe ta INEC ta fara tura sakon training ta Email ga wadanda suka cike aikin na zaben da za a gunadar a shekarar 2023. A sakon hukumar tana bukatar mutum ya bi wani link da take turowa domin ya zabi training center

Wadanda ba su cike wannan aiki na zabe ba har yanzu suna da damar cikewa. Za ka iya shiga rubutun da ke kasa domin cike aikin na zabe.

Yadda Zaka Cika Aikin zabe

A yanzu haka wannan INEC ta fara tura wannan sako na training center, ta fara turawa Jihar Bauchi kamar yadda za ku gani a nan kasa

Hukumar tana kan wannan aikin na tura sako ta Email, saboda haka duk wanda ya cike ya jira za su turo masa, suna turo ma ka shiga ka cike training center mafi kusa da kai. Saboda idan ba ka yi hanzari ka cike da wuri ba har center ta cika za su tura ka inda suka ga dama ne.

Sannan kuma ga wanda ba su cike wannan aiki na zabe ba har yanzu suna da damar cikewa. Za ka iya shiga rubutun da ke kasa domin cike aikin na zabe.

Yadda Zaka Cika Aikin zabe

Allah ya bada sa’a

Advertisement Join Our Whatsapp Group Join Our Whatsapp Group

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button
error: Alert: Content selection is disabled!!