Ga Wata Sabuwar Dama Ta Samu: DanGote Zai Dauki Matasa 300,000 Aiki A Fadin Nigeria

Assalamu Alaikum Jama’a barkanmu da wannan lokaci sannunmu da sake kasancewa daku a wannan shafin namu namu mai albarka hikimatv.com
Dangote zai fara shirin daukar ‘yan Najeriya 300,000 aiki a karkashin shirinsa na rage zaman kashe wando a kasar Sabon shirin na daukar ‘yan Najeriya aiki a kamfanin Dangote zai kasance ne a karkashin kamfanonin sukari da man fetur Aikin da za a ba ‘yan Najeriya a karkashin matatar man Dangote a Legas zai hada da wurin zama ga ma’aikata 20,000.
Aliko Dangote ya sanar da kirkirar ayyuka 300,000 sabbi ga ‘yan Najeriya a shirinsa na sake zuba jari a kamfanin sukarinsa. Wannan daukar aiki mai yawa an sanar dashi ne a cikin wata sanarwa da kamfanin ya fitar, kamar yadda rahotanni suka bayyana.
A cewar rahoton Punch, an naqalto shugaban kamfanin, Aliko Dangote na cewa, zai fadada fannin samar da sukari da kuma kudade shiga ne ga kamfanin.
Wannan shiri nasa na zuwa ne bayan da ya bayyana sabon kudurin daukar aiki a matatar man fetur dinsa da ke Legas.
Karanta Wannan: Har Yanzu Ana Iya Cike Tallafin Rancen Kudi Daga Gomnati Ga Jerin Rancen Kudin Da Har Yanzu Suna Tafiya
Attajirin mafi kowa kudi a Afrika ya ce damammakin aikin za su hada da ayyukan kai tsaye da ku ma fakaice. Ya kuma bayyana cewa, mafi yawa a daukar aikin zai kasance ne a fannin sarrafa sukarinsa da ke jihar Adamawa.
Yadda Dangote ze ba da gudunmawa wajen rage zaman banza
Kamfanin simintin Dangote, daya daga cikin kamfanonin da Aliko Dangote ya mallaka na daga cikin kamfanonin da ke samar da ayyukan yi a Afrika.
Yawan sanar da ayyukan kamfaninsa yasa aka nada shi shugaban kwamitin samar da ayyukan yi a gwamnatin Najeriya. An ba shi wannan matsayin ne saboda samar da ayyuka da ya yi ga ‘yan Najeriya da dama.
Karanta wannan Shin Ta Yaya Madatsa Da Yan Damfara Suke Samun Bayanan Mutun
A cewar ma’aikatar masana’antu da zuba hannun jari, matatar man Dangote za ta samar da ayyuka sama da 250,000 idan aka kammala ta.
Ga Masu Sha’awar Cika Wannan aikin saiku danna Link dake kasa domin Cikawa
Click Here To Apply
Allah ya bada Sa’a