Ga Wata Sabuwar Dama Ga Matasan Nigeria Daga Hukumar NiTDA

HUKUMAR (NITDA) ZA TA BA DA HORAR GA ƳAN NAGERIYA MUTUM (MILIYAN ƊAYA 1)

Assalamu alaikum jama,a Barkanku da wannan lokaci da fatan kowa Yana Cikin koshin lpy.

Hukumar bunƙasa fasahar sadarwar zamani ta ƙasa, (NITDA), ta ƙarƙashin cibiyar ƙere-ƙeren na’urorin zamani, “National Center for Artificial Intelligence & Robotics,” (NCAIR), za ta ba wa ƴan ƙasa horo akan yadda ake ƙera na’urorin fasahar zamani, gami da yadda ake sarrafa su.

Horon wanda za a gudanar shi rukuni-rukuni, na zaman wani fanni na wani shiri na musamman da hukumar ta (NITDA), ta tsara domin horar da ƴan Nageriya mutum miliyan 1.

Wannan wata dama ce ga duk wani ɗan ƙasa wanda ya kai shekaru 15 a duniya, ya ke kan karatun sakandire ko digiri ko ya ke kan aikin yi wa ƙasa hidima (NYSC), da duk wani wanda ya ke da sha’awar samun horo kan fasahar zamanin, abin duba dai, horon a zahiri ne a birnin Abuja.

Danna Link din Dake Kasa Domin cikawa

Click here to Apply

Allah ya bada Sa’a

Advertisement Join Our Whatsapp Group Join Our Whatsapp Group

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button
error: Alert: Content selection is disabled!!